Tarihin haduwar Bournemouth da Manchester City

'Yan wasan Bournemouth da Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ta lallasa Bournemouth da karin kwallaye hudu cikin wasanni ukku da suka buga a gasar Primiya

Kafin haduwar tasu ta ranar Litinin mai masaukin bakin tana matsayi na 14 a tebur da maki 26, yayin da Manchester City ke matsayi na biyr da maki 49.

Manchester City ba ta taba rashin nasara a hannun Bournemouth ba a gasar lig, sai dai ma ta doke ta sau 7 kuma suka yi canjarsa sau 2.

Manchester City ta doke kungiyar a dukkanin wasanninsu uku na Premier, inda ta zura mata kwallo 13, ita kuma ta jefa wa City kwallo daya kawai a raga.

Matsayin Bournemouth kafin wasanta da City

Bournemouth ta yi wasa hudu ba tare da ta yi nasar ba a wasan Premier a gida tun bayan da ta doke Leicester 1-0 ranar 13 ga watan Disamba, inda ta yi canjaras biyu kuma ta yi rashin nasara biyu.

Bournemouth ba ta yi nasara ko daya ba a dukkanin wasanninta a 2017, inda ta yi canjaras biyu, ta sha kashi sau hudu.

Kungiyar za ta iya kasancewa ba ta yi nasara ba ko daya a wasanninta shida na farko na lig a shekara, a karon farko tun 1960 lokacin tana gasa ta uku.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

An zura wa kungiyar kwallo 16 a raga a gasar Premier a 2017, inda ta fi sauran kungiyoyi da kwallo hudu.

Kungiyar tana da maki 26 bayan wasannin Premier 24, sabanin maki 28 da ta samu a irin wannan lokaci a bara.

Southampton ce kadai (ta 17 a tebur ) ta yi rashin maki a matsayin da take na samun nasara, fiye da Bournemouth (ta 15 a tebur) a gasar Premier a bana.

Matsayin Manchester City kafin wasanta da Bournemouth

Ba a doke Manchester City ba a wasanninta hudu gaba daya, tun bayan da Everton ta doke ta da ci 4-0, inda ta yi nasara a ukuta yi canjaras a gud daya.

Ta yi rashin nasara a wasanninta biyu daga cikin tara na Premier, amma rashin nasarar biyu ta yi ne a wasanninta uku na waje.

Gabriel Jesus ya ci kwallo a dukkanin wasanninta biyu na Premier da ya fara bugawa.

'Yan wasan da suka taba ci wa City kwallo a wasanninsu uku na farko na Premier su ne Emmanuel Adebayor (hudu a 2009) da Kevin de Bruyne (uku a 2015).

De Bruyne ya bayar da kwallo sau tara aka ci a gasar Premier a bana, kuma tun lokacin da suka ci Arsenal 2-1 ranar 18 ga watan Disamba bai kara taimakawa ba an ci.

Manchester City ta yi nasara a wasa 10 daga cikin 12 wadanda aka fara sanya mai tsaron ragarsu Willy Caballero a bana, inda suka yi canjaras a guda daya, kuma aka ci su a daya, sabanin 11 da suka yi nasara daga cikin 23, lokacin da suka sa golansu Claudio Bravo, inda suka yi canjaras a 6, aka ci su a 6.