Buhari na shan addu'a a coci-coci da masallatai

Nigeria
Image caption Wasu mabiya addinin Kirista a Maiduguri yayin da suke yi wa shugaba Buhari addu'o'i

An fara gabatar da addu'o'i na musamman a wasu sassan Najeriya don rokon Allah ya bai wa shugaban kasar, Muhammadu Buhari, lafiya.

A ranar 19 ga watan Janirun da ya wuce ne dai shugaba Buhari ya tafi hutu tare da ganin likita a Birtaniya.

Amma a makon jiya ne kuma ya sake aika wa majalisar dokokin kasar takardar neman tsawaita hutun da zummar kammala gwaje-gwajen lafiyarsa.

Lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar, inda wasu ke ganin akwai ayar tambaya a kan lafiyar shugaban, sai dai fadar gwamnati ta musanta zargin tana mai cewa lafiyar shugaban kalau yana dai jiran sakamakon wasu gwaje-gwaje da aka yi masa ne.

Ci gaba da kasancewarsa a London ba tare da cikakken bayanin abin da ke damun Mr. Buhari ba yasa wasu coci-coci da ke kasar suka umarci mabiyansu da su fara addu'o'i na musamman na tsawon mako guda don nema wa shugaban lafiya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ma kusan masallatai 350 ne suka yi wa shugaban addu'o'in neman samun sauki a jihar Borno da ma wasu sassan kasar.

Image caption Wasu mabiya addinin Musulunci a Maiduguri yayin da suke yi wa shugaba Buhari addu'o'i

Shi ma sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar da sarkin Ilorin, Alhaji Sulu Gambari da kuma gwamnan jihar Osun da ke Kudancin kasar, Mista Rauf Aregbesola, sun jagoranci gabatar da addua'a ta musamman a ranar Lahadi, wadda kungiyar al'ummar Musulmai ta jihar Osun ta shirya.

Shugaba Buhari na ci gaba da kasancewa a Burtaniya ne a yayin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki da aka shafe shekaru da dama ba a ga irinsa ba.

Abin da ke ci gaba da sanya damuwa a zukatan miliyoyin 'yan kasar.