Kashi 39 cikin 100 na 'yan wasan a Ingila ba a yi musu gwaji ba

drugs

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin sinadaren karin kuzari

Hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta Ingila, ba ta yi wa akalla kashi 39 cikin dari na 'yan wasan kwallon kafa da suka yi wasa a Ingila a bara gwaji ba, kamr yadda alkaluma suka nuna.

Hukumar (Ukad) wadda ke gudanar da gwajin a madadin hukumar kula da kwallon kafa ta Ingila, ta debi abubuwan da ake gwajin da su 1,204, dag 'yan wasa 1,989 da za su yi wasa a kakar wasan kwallon kafa ta Ingila ta 2015-16.

An debi abubuwan gwaji 799 a jikin 'yan wasa 550 da za su yi wasa a gasar Premier. Amma kuma ba a gudanar da gwajin a kan 'yan wasa gasar kasa ta Ingila ba.

Wadannan alkaluman ba su hada da 'yan wasan da aka yi musu gwajin fiye da sau daya ba.

Wannan na nufin za a samu abubuwan gwaji biyar a kan dan wasa daya da aka yi wa gwaji sau biyar, yayin da wasu abubuwan gwajin da aka tattara daga wasu 'yan wasan da suka yi rijista da kungiyoyi, amma kuma ba a sa su a wasa sosai.

Alkaluman da aka fitar sun nuna abubuwan gwaji 36 kawai aka dauka daga 'yan wasa 169 da za su yi wasa a babbar gasar kwallon kafar mata ta Ingila.

Hakan na nufin ba a yi wa 'yan wasa 78 cikin dari gwajin ba kenan.

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce, kamar a sauran wasanni, tana bayar da fifikon gudanar da gwajin amfani da abubuwan kara kuzari a kan 'yan wasan da ke babbar gasarta.