Indonesia: An hana dalibai bikin ranar Valentine

Valentine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ranar 14 ga watan Fabrairu ne masoya a fadin duniya suke bikin wannan rana ta Valentine

Hukumomi a wasu bangarori na Indonesiya sun haramtawa dalibai gudanar da bikin ranar Valentine, suna mai cewa hakan yana karfafa gwiwar yin zinace-zinace.

A birnin Makassar, 'yan sanda sun kai samame shaguna inda suka lalata kwaroron roba da ke cikin kantunan.

Magajin garin yankin ya shaida wa BBC cewa, an kwashe kwaroron robar ne bayan da mutane suka gabatar da korafe-korafe, kuma ba za a ci gaba da sayar da shi a fili ba.

A birnin kasar na biyu mafi girma kuwa Surabaya, an hana dalibai yin bikin ranar, inda jami'an gwamnati suka ce ranar Valentine ta sabawa al'adu da dabi'un kasar.