India ta harba katafaren kumbo sararin samaniya

India Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Indiya ta kuma bayar da sanarwar shirye-shiryen da take yi na zuwa duniyar Venus

Kasar Indiya ta kafa tarihi sakamakon nasarar da ta yi na harba katafaren kumbo mai dauke da tauraron dan adam 104 a karon farko, inda ta wuce Rasha wadda ta kaddamar da nata kumbon mai tauraron dan adam 37 a shekarar 2014.

Dukkan tauraron dan adam din na kasashen waje ne in ban da uku daga ciki, kuma mafi yawansu na Amurka ne.

An kaddamar da harba kumbon ne a tashar sararin samaniya ta Sriharikota a Kuduncin kasar.

Masu lura da al'amura sun ce wannan abu na nuna cewa Indiya tana tasowa don zama mai taka muhimmiyar rawa a safara zuwa sararin samaniya na dumbin biliyoyin daloli.

Daraktan wannan aikin ya ce, "Wannan lokaci ne na musumman ga al'ummar kasar. Yau mun kafa tarihi."

India za ta harba tauraro duniyar Mars

Firai minista Narendra Modi, na daya daga cikin wadanda suka fara taya masana kimiyya murnar wannan nasara inda ya rubuta a shafinsa na Twitter, "Wannan nasara da @isro ta yi, wani abin alfahari ne ga bangaren kimiyyar sararin samaniyar kasarmu baki daya. Indiya tana jinjinawa masana kimiyyarta."

Daga cikin kananan taurarin dan adam 104 din, 96 na kasar Amurka ne, sauran kuwa na Isra'ila da Kazakhstan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Switzerland da kuma Netherlands ne.

Gwamnatin Indiya ta kara yawan kudaden da take sawa a harkar safara zuwa sararin samaniya a kasafin kudinta na wannan shekara.

Tun shekaru 20 da suka gabata Indiya ke taka rawa cikin kasashen da suke harkar safara zuwa sararin samaniya wadda ke kawo makudan kudi

Labarai masu alaka