An zuzuta yawan kudin jabu a Nigeria — CBN

CBN
Image caption Kudaden na Asusun-Bai daya dai na Babban Bankin Najeriya wato CBN

Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce, kudaden jabu da ke yawo a hannun al'umma ba su kai kaso daya ba, sabanin kaso 20 da ake yayatawa.

A wata sanarwa da banki ya aike wa BBC, bankin ya ce duk da cewa babu wata kasa da kudinta suka gagari gogayya da na jabu, babu irin wadannan kudaden na jabu da ke zagayawa a Najeriya, da yawa.

Bankin ya kara da cewa "kididdigar bankin daga Janairu zuwa Disambar 2016, ta nuna cewa akwai kudaden jabu da yawansu bai kai kaso daya ba."

CBN ya ce kaso daya na nufin za a iya samun jabun takardun kudi guda 14 daga cikin Miliyan daya.

A ranar Talata ne dai BBC ta wallafa wani labari, a inda tsohon mataimakin gwamnan babban banki, Dr. Obadiah Mailafia, ya shaida wa wani kwamitin Majalisar Wakilan kasar, cewa jabun kudi sun kai kaso 20 a Najeriya.

A cewarsa ma'aikatan babban bankin kasar na hada baki da bankunan kasuwanci domin sake dawo da kudaden da suka tsufa cikin sha'anin hada-hadar kudi.

Dr Mailafiya ya ce, "idan kudade suka tsufa a kan tara su ne a kone, sannan a kera wadanda za su maye gurbinsu."

Mailafiya ya kara da cewa "Amma akan samu ma'aikatan babban banki da ke hada baki da bankunan kasuwanci wajen sake mayar da kudin cikin harkokin kasuwanci."

Tsohon mataimakin shugaban babban bankin na najeriya, ya kuma ce, an shafe fiye da shekara ana yin hakan, yana mai cewa idan aka ci gaba da wannan cuwa-cuwa babu ta yadda Naira za ta sake samun tagomashi a kan Dala.

Bisa tsarin dokar hada-hadar kudade dai, ana yi ayyana kudaden da suka tsufa sannan aka hana su kai komo a tsakanin mutane, da na jabu.