'Yadda Boko Haram suka yanka mijina da 'ya'yana hudu'

'Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin Najeriya na cigaba da fafatawa da kungiyar Boko Haram a yankunan jihar Borno

Wata mata wadda 'yan kungiyar Boko Haram suka yanka mijinta da 'ya'aynta guda hudu ta labarta wa BBC yadda al'amarin ya wakana.

Matar ta ce 'yan kungiyar sun je suka buga mata kofar daki har ma suka karya ta.

Ta ce sun shiga kai tsaye zuwa dakinta, bayan da suka karya kofar dakin sannan suka fito da ita waje.

'Yan kungiyar sun dai je gidan matar ne da nufin kashe mijinta, a inda suka yi ta harbinta domin fada musu wurin da mai gidan nata yake.

Ga dai ci gaban yadda hirar matar ta kasance da Bilkisu Babangida:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda Boko Haram suka yanka mijina da 'ya'yana