Wata tsohuwa mai shekara 64 ta haifi tagwaye

An old woman has given birth to a twin

Asalin hoton, ReCOLETAS HOSPITAL VIDEO SCREENGRAB

Bayanan hoto,

Asibitin ya nuna wani ɓangare na tiyatar da aka yi wa tsohuwa

Tsohuwa mai shekara 64 ta haifi tagwaye - namiji da mace - cikin ƙoshin lafiya a Burgos da ke arewacin ƙasar Spaniya.

Sai da aka yi wa matar tiyata kamar yadda aka saba yi a irin yanayi na ba sabon ba.

Asibitin ya wallafa hoton bidiyon tiyatar da aka yi wa tsohuwar wadda ta haihu ba tare da wata matsala ba.

Shekara biyar da ta wuce ma, matar ta haifi 'ya mace.

Asalin hoton, RECOLETAS HOSPITAL VIDEO SCREENGRAB

Bayanan hoto,

An nuna hoton ɗaya daga cikin jariran tsohuwar jim kaɗan bayan haihuwarsu

An ba da rahoton cewa tagwayen da mahaifiyarsu na cikin ƙoshin lafiya a asibiti, nauyin namijin ya kai kilogram 2.4, macen kuma kilogram 2.2.

A shekarun baya-bayan nan, kafar yaɗa labarai ta El Pais ta ruwaito cewa an samu wasu mata Spaniyawa biyu da su ma suka haihu a shekarunsu na 60.

Haka ma a watan Afrilun 2016 wata dattijuwa a ƙasar Indiya Daljinder Kaurta haifi lafiyayyen jaririnta a shekarunta na 70, a jihar Haryana.