Blair ya ce 'yan Burtaniya su sake tunani kan ficewa daga EU

Tony Blair

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Blair ya ce ko da yake kashi 52 cikin 100 ne suka zabi ficewa, amma sai a duba batun sannan a sake ba da damar yin tunani

Tsohon fira ministan Burtaniya Tony Blair ya ce aniyarsa ita ce ya rarrashi 'yan kasar don su dawo daga tunanin barin Tarayyar Turai.

Blair ya yi iƙirarin cewa mutane sun kaɗa ƙuri'a ne a zaɓen raba gardama "ba tare da sanin haƙiƙanin abin da ke tattare da barin Tarayyar Turai ba".

Don haka ya buƙaci "wata mafita daga ruguguwar da ake yi, ta ci gaban mai shiga daji".

Tsohon shugaban jam'iyyar Conservative, Iain Duncan Smith ya ce kalaman Tony Blair akwai nuna isa kuma ba su dace da dimokraɗiyya ba, sai dai Mr Nick Clegg na jam'iyyar Liberal ya ce ya "amince da kalaman".

Tsohon shugaban jam'iyyar UKIP, Nigel Farage ya ce Blair "mutumin da ne" yayin da fadar Downing Street ta ce ta "duƙufa gaba ɗaya" wajen tabbatar da cikar burin fita daga Tarayyar Turai.

Sakataren wajen Burtaniya Boris Johnson ya kara da cewa: "Ina kira ga al'ummar Burtaniya su tashi su kashe talbijin nan gaba idan Blair ya sake bijiro musu da wannan raini."

Fira minista Theresa May na son bijiro da tattaunawa a hukumance kan ficewar Burtaniya a ƙarshen watan Maris - wani mataki da ya samu goyon bayan majalisar wakilan ƙasar a makon jiya.

Bayanan hoto,

Theresa May za ta bijiro da batun tattaunawa a kan batun ficewar Burtaniya a watan gobe

'damar sake tunani'

Tony Blair, wanda ya jagoranci Burtaniya a tsakann 1997 zuwa 2007, ya yi amfani da wannan jawabi a wani taron ƙungiyar gangamin goyon bayan zama a Turai wajen musun cewa barin Tarayyar Turai zai yi "ciwo" ga Burtaniya da Turai kuma amfanin abin "galibi mafarki" ne kawai.

Tsohon fira ministan wanda ya yi yaƙin neman ci gaba da zama a Tarayyar Turai, ya ce yayin da ya amince cewa mutane sun kaɗa ƙuri'ar ficewa da rinjayen kashi 52 a kan masu son a zauna kashi 48, ya ba da shawarar sake duba a kan ficewar Burtaniya lokacin da "muke da fahimtar inda muka dosa".

"... wannan batu, wata shawara ce guda mafi muhimmanci da ƙasar nan ta ɗauka tun bayan Yaƙin Duniya Na biyu kuma ba za a iya rufe damar ci gaba da muhawara game da batun a yanzu ba."