Ko gawar Mugaba ce take takara za ta ci zabe - Grace

Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robert Mugabe ya samu amincewar jam'iyyarsa don ya sake tsaya wa takara a zabe mai zuwa

Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe Grace Mugabe ta ce maigidanta na da tsananin farin jini a wajen masu kada kuri'a ta yadda ko gawarsa ce ta tsaya takara za ta ci zabe.

Mai dakin Robert Mugaben na wannan jawabi yayin wani gangami da jam'iyyar ZANU-PF mai mulki ta shirya.

Robert Mugabe mai shekara 93, ya bayyana aniyarsa karara ta tsaya wa zaben wanda za a yi shekara mai zuwa.

Grace mai kimanin shekara 51 fitacciyar mai suka ce ga mutanen da ke nuna sha'awarsu ta gadon mijinta.

Mugabe ya fara mulkin Zimbabwe tun bayan kawo karshen mulkin gwamnatin farar fata a 1980 bayan gwabza wani kazamin yaki.

Matarsa, wadda sau da yawa ke bayyana biyayyar mutu-ka-raba ga shugaba Mugabe, tagomashinta na kara fitowa a wajen jama'a.

Ta ce"wata rana, idan Allah ya kaddara mutuwar Mugabe, za mu sanya gawarsa a matsayin 'yar takara a cikin takardar kuri'a."

Labarai masu alaka