US: Gwamnatin Trump ta gargadi Russia kan Ukraine

Mike Pence mataimakin Donald Trump
Bayanan hoto,

Mike Pence ya nemi Russia ta martaba Ukraine

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya fada wa mahalarta taron kasashen duniya a birnin Munich na Jamus cewa, Russia ce ke da alhakin duk abin da ke faruwa a gabashin Ukraine da kuma hade Crimea da ta yi da kasarta.

A jawabinsa na farko a wata kasa, Mista Pence, ya gargadi Russia da ta martaba yarjejeniyar da aka cimma a 2015 ta tsagaita wuta.

Sai dai kuma Mike Pence ya ba da tabbacin cewa sabuwar gwamnatin Amurka za ta yi kokarin cimma daidaito dangane da rikicin.

Mista Pence ya kara da bayyana ci gaba da kawance da Kungiyar Tsaro ta NATO, amma kuma ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kara yawan kudaden da suke kashewa kan tsaro.

Ana dai ganin kamar sabuwar gwamnatin Amurka ba ta da karsashin da za ta iya yi wa Russia irin wannan kalamai.

Ana dai zargin Russia da yin kutse lokacin zaben Amurka abin da ya ba wa shugaba Donald Trump nasara bisa abokiyar karawarsa, Hillary Clinton.

Tun ma kafin zaben, an jiyo mista Trump yana bayyana shugaban Russia, Vladimir Putin da shugaban da ya fi shugaban Amurka na lokacin, Barack Obama.

Ko a baya-bayan nan ma dai sai da aka yi ta kai-ruwa rana tsakanin shugaba Trump da Hukumomin tsaron kasar kan rawar da Russia ta taka wajen yi wa Amurkar kutse a lokacin babban zaben kasar.