Kun san abin da dalolin Andrew yakubu za su iya yi a Nigeria?

  • Usman Minjibir & Halima Umar Saleh
  • BBC Hausa
Andrew Yakubu

Asalin hoton, Encyclopedia

Bayanan hoto,

Andrew Yakubu ya rike matsayin shugaban NNPC daga shekarar 2014 zuwa 2014

A makon da ya gabata ne dai Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya ta ce ta samu dalar Amurka miliyan 9.5 da kuma fam na Ingila 78,000 a wani gida mallakar tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC, Andrew Yakubu.

Kwatankwacin hakan dai a kasar shi ne fiye da Naira biliyan hudu.

Hukumar dai ta ce ta samu makudan kudaden ne makare a cikin wasu akwatuna masu sulke wadanda wuta ba ta cin su a wani gida a kudancin jihar Kaduna.

Shugaban Hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu, ya shaida wa BBC cewa "Abin mamaki gidan da aka ajiye wannan kudi gabadayansa bai kai naira miliyan biyar ba."

Yanzu dai wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta mallaka wa gwamnatin kasar naira biliyan ukun da aka gano a gidan.

Hakan ya biyo bayan bukatar da hukumar EFCC ta shigar a gaban kotun.

Wadanne abubuwa kudin Andrew Yakubu za su iya yi wa Najeriya?

Tun dai bayan wannan samame da hukumar ta EFCC ta kai, 'yan kasar ke ta faman kumfar baki da neman sanin hakikanin yawan kudin da kuma abin da za a iya yi da su.

Yawan abin da aka samu a kudin Najeriya ya kai fiye da naira biliyan uku.

Masana harkar kudi da na tattalin arziki sun ce kudaden ka iya taimaka wa kasar wajen magance wasu matsalolin da take fama da su, musamman wajen aiwatar da ayyukan ci gaba kamar gina tituna da gadoji da asibitoci da dai sauransu.

Ina sauran kudaden da aka kwato?

Baya ga Andrew Yakubu, hukumar EFCC ta ce ta samu irin wadannan kudade da ke shan boyo a wurin tsofaffin jami'an gwamnati da dama.

"Akwai wani ma'aikacin gwamnati da muka kwato naira biliyan daya da miliyan dari biyar [a wurinsa]", in ji Ibrahim Magu.

Mista Magu ya ci gaba da cewa, "Fisabilillahi, muna kwato kudade fa, kusan kullum, daga asusun mutane, sannan akwai ma wadanda suke amincewa da su kawo kudin bisa radin kansu."

Dangane kuma da yawan kudaden da EFCC ta kwato daga hannun mazambata, Ibrahim Magu ya ce hukumar ta karbo makudan kudin da ba zai iya kawo adadinsu ba da ka.

Sai dai ya ce ana mayar da kudaden ne zuwa ga lalitar gwamnati domin da ma mallakarta ne.

Bayanan hoto,

Ibrahim Magu yana fuskantar kalubale

Me ake yi da kudaden?

'Yan Najeriya dai na korafin cewa ana ta kwato makudan kudade daga mutanen da suka karya arzikin kasar, amma har yanzu ba su gani a kasa ba.

Wasu dai na ganin ya kamata a zuba kudaden wajen tayar da komadar da kasar ta fuskanta ta fannin tattalin arziki.

Sai dai kuma shugaban na EFCC, Ibrahim Magu, ya ce akwai hanyoyin shari'a da sai gwamnati ta bi su sannan ta yi amfani da kudaden wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

To amma, a cewar Mista Magu, nan da watanni uku 'yan Najeriya za su iya sanin yawan kudaden da hukumar ta amso da kuma yadda gwamnati za ta kashe kudaden.

Yadda ake gano barayin gwamnati

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tun dai bayan albishir din ba da tukwici da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi ga duk mutumin da ya fasa-kwai ko kuma ya fallasa jami'an da suka yi wa kasa ha'inci, hukumar EFCC ta ce tana ta samun nasarar kamu.

A watan Disamban 2016 ne dai ministar kudin Najeriya, Kemi Adeosun, ta sanar da sabon tsarin, wanda ta ce wata sabuwar hanya ce ta yaki da rashawa da cin hanci a kasar.

Ministar ta ce masu fasa-kwai za su sami tukwicin kashi biyu da rabi zuwa biyar cikin dari na kudaden da aka kwato.

Ibrahim Magu ya ce sun sami bayani daga masu irin wannan fallasa kuma sun yi aiki a kai, al'amarin da ya kai ga gano abin da aka samu a hannun tsohon shugaban NNPC Andrew Yakubu.

Gwamnatin Buhari kan Cin hanci da Rashawa

Tun a lokacin yakin neman zabe Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi ta nanata batun yaki da cin hanci da ya yi wa kasar dabaibayi.

Wannan ne ma daya daga cikin dalilan da wasu ke tunanin suka sa 'yan Najeriyar fitowa kwansu da kwarkwata wajen zaben Buhari a matsayin shugaban kasa.

Kuma ko a lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki, Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa.

Irin wannan kamu da hukumar EFCC ke yi na daya daga cikin hanyoyin yaki da rashawa da cin hanci musamman a tsakanin jami'an gwamnati.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ki cewa uffan kan batun rikici APC

Sai dai kuma wasu masu sharhi na ganin beken tsarin da aka bi wajen tafiyar da yakin.

Wasu dai na ganin cewa babu yadda za a yi ma'aikacin gwamnati ya daina dibar arzikin kasa, bayan albashinsa bai taka kara ya karya ba, musamman a lokacin tsadar kayayyakin masarufi.

Masu hamayya da jam'iyya mai mulki wato APC na ganin yaki da cin hancin wata kafa ce ta yi wa 'yan adawa bi-ta-da-kullin siyasa, saboda a cewarsu 'yan adawar kawai ake kamawa.

Akwai kuma masanan da ke ganin cewa nasarar yaki da cin hanci a Najeriya ta ta'allaka ne kawai ga gyaran kundin tsarin mulkin kasar domin tanadar hukunci mai tsanani a kan duk wanda aka samu da hannu dumu-dumu.

Batun cin hanci a Najeriya dai ya zama ruwan dare kuma ya samu karbuwa shekara da shekaru.

Masana tattalin arziki dai na yi wa rashawa da cin hanci kallon hanyar da ta sanya tattalin arzikin Najeriya ya zagwanye.

Kuma a cewarsu, da za a karbo kudaden sannan a jefa su cikin asusun gwamnati domin aiwatar da ayyukan ci gaba, to da Najeriyar ta zama wata sabuwar duniya.