An Sake Rantsar da Shugaba Adama Barrow na Gambia

Asalin hoton, Reuters
Adama Barrow na gaisawa da dubban magoya bayansa a filin wasa na Independence
An sake rantsar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambia bayan wata takaddamar siyasa.
Mr Barrow ya sha rantsuwar kama aiki ne a wani filin wasa inda jama'a suka yi dafifi, a Banjul babban birnin kasar.
Cincirindon jama'ar sun yi sowa yayin da ake kade-kade da bushe-bushe, yayin da shi kuma ya taka sannu a hankali, ya hau kan dandamalin dake tsakiyar filin wasan.
A watan Janairu ne dai magabacinsa, Yahya Jammeh, ya sauka daga mukamin na shugaban kasa, bayan da ya sha kaye a zaben shugaban kasa, kana aka yi barazanar tumbuke shi da karfin tuwo lokacin da ya ce ba zai sauka ba.
Dama dai an rantsar da shugaba Adama Barrow a karon farko a wani kwaryakwaryar biki a kasar Senegal mai makwabtaka, saboda da a lokacin yana fargabar abinda zai iya faruwa da shi idan ya tafi kasar Gambia.
A halin yanzu dai Yahya Jammeh na gudun hijira a kasar Guinea Conakry.