Wasu karin sojojin sudan ta Kudu sun yi murabus

Shugaba Salva Kiir
Bayanan hoto,

Rikicin da kasar Sudan ta Kudu ta fada, ya haddasa mutuwar daruruwan 'yan kasar da tserewar wasu daga kasar baki daya.

Manyan jami'an soji a gwamnatin Sudan ta Kudu, sun sanar da yin murabus daga aiki, bayan sun zargi shugaba Salva Kiir da hannu a yakin basasa da kabilancin da kasar ta samu kan ta a ciki.

Daya daga cikin jami'an uku Birgediya Henry Oyay Nyago, ya zargi shugaba Kiir wanda ya fito daga kabilar Dinka, da ba da izinin kashe duk wani farar hula da ba kabilarsa ba.

Ya yin da Kanal Khalid Ono Loki, ya zargi shugaban hafsan sojin kasar da kamewa da garkame wadanda ba 'yan kabilar shugaban kasar ba.

A makon da ya gabata Laftanal Kanal Thomas Cirillo Swaka, ya mika tashi takardar yin murabus din, bayan zargin shugaba Salva Kiir da kokarin share duk kabilar da ta bata shi ba a Sudan ta Kudun.

Sai dai kawo yanzu, babu wani martani da sojojin kasar ko gwamnati suka maida kan wadannan zarge-zarge.

Matakin tsige mataimakin shugaban kasa Riek Machar daga mukaminsa da shugaba Salva Kiir ya yi, ya kara haddasawa kasar fadawa yakin basasa.

Ko bayan wata daidatawar wucin gadi da aka yi dan tabbatar da zaman lafiya a kasar, mista Machar din ya ki komawa kasar saboda rashin tabbas din tsaron lafiyar sa.