Iraqi ta fara 'samun galaba' kan IS a Mosul

Dakarun sojin Iraqi
Bayanan hoto,

Tun bayan hambarar da gwamnatin marigayi Saddam Hussain, kasar Iraqi ta fada cikin yaki da 'yan tawaye da mayakan IS

Sojojin Iraqi sun fara kai hare-hare a kan 'yan kungiyar IS da ke yammacin birnin Mosul da manufar sake kwato yankin daga hannun mayakan.

Daruruwan motocin yaki ne dai bisa rakiyar jiragen yaki na sama, suka kutsa yankin da safiyar Lahadi.

Tun da sanyin safiyar Lahadin ne dai sojojin Iraqin suka karbe kauyuka da dama da ke kusa da birnin.

Wani janar din sojan kasar, Abdulamir Yarallah, a wata sanarwa, ya ce, an kama kauyuka guda biyu da suka hada da Athban da Al-Lazzagah da ke kudu da filin jirgin Mosul.

Firai ministan Iraqi, Haider al-Abadi ne dai ya bude kai hare-haren.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ya zama dole dakarun na Iraqi su tabbatar da tsaron lafiyar daruruwan fararen hula da ke cikin birnin.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a kasar, Lise Grande ya shaida wa BBC cewa, ya zama dole dakarun gwamnati su tabbatar da kare 'yan kasar domin haka na daga cikin nasara a ayyukan da suka sanya a gaba.