Trump ya wa 'yan jarida shagube a Florida

Trump na jawabi a taron Florida
Bayanan hoto,

Shugaba Donald Trump na Amurika

Shugaba Trump ya yi wa 'yan jarida shagube ,a wurin taron da ya gudana a Melbourne a jihar Florida.

Ya furta cewa, 'yan jarida basu san fadar gaskiya a game da aikin su na rahoto,suna da wata ajadarsu ta daban.

Mista Trump ya sanar da cewa ,ya zo Florida sabili da ya son ya kasance cikin abukanshi ,cikin jama'a.

Kungiyar da ta jagorenci yakin neman zaben shugaban, ita ce ta shirya wannan taro ba fadar White House ba.

Kakakin shugaban,Sarah Huckabee Sanders ta danganta wannan taron da yakin neman zabe a Amurka. Ta na mai cewa, Trump na son ya yi magana da jama'a karara, kuma kai tsaye.

Tun dai ranar asabar ne, Trump ya aika da sako a shafin sa na Tweeta ,inda ya ke cewa ya na jiran ya ga dandazon jama'a sun halarci wurin taron.