Harin kunar bakin-wake ya kashe mutum 19 a Somalia

Al-Shabab

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Al-Shabab tana adawa da gwamnatin Somalia

Mutane akalla 19 sun mutu sannan kuma wasu da dama sun jikkata sanadiyar wani harin kunar-bakin wake a Mogadishu, babban birnin Somalia.

Rahotanni na cewa an kai harin bam din ne da mota, a wata karamar kasuwa da ke bakin titi ranar Lahadi da safe.

Wadanda suka shaida yadda al'amarin ya faru sun ce ga alama bam din na da girma sosai saboda da irin karar fashewar da suka ji.

Jami'ai a wani asibiti a birnin na Mogadishu, sun ce sun karbi mutane 47 da suka samu raunuka sakamakon harin.

Wannan dai shi ne hari na farko, tun bayan zaben shugaban kasar, Mohammed Abdullahi Mohammed, a watan da ya gabata.

Jiya wani kwamandan kungiyar masu ikirarin kishin Islama ta Al-Shabab, wadda ta dade tana kai hare-hare a kasar ta Somalia, ya sha alwashin kai hari ga duk wanda ya bai wa sabon shugaban kasar hadin kai.

Ya bayyana shugaban a matsayin mai ''muguwar aniya'' .

Kawo yanzu kungiyar ta al-Shabab bata dauki alhakin kai harin ba.