Har yanzu babu wanda ya dace ya gaji kujerata — Mugabe

Robert Mugabe
Bayanan hoto,

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe yana mulki tun 1987

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, ya ce, jam'iyyarsa ta ZANU PF da kuma jama'ar Zimbabwe, ba su ga wani nagartaccen mutum da ya dace ya gaje shi a shugabancin kasar ba, a manyan zabukan da ake shirin yi a 2018.

A wata hira da kafar watsa labarai ta gwamnatin kasar gabanin ranar cikarsa shekara 93, Mugabe, ya ce, galibin 'yan Zimbabwe ba su ga mutumin da ya dace ya maye gurbinsa a matsayin shugaban kasar ba.

Tun dai 1980 shugaban ke mulkin Zimbabwe.

A watan Disamban da ya gabata, jam'iyyar ZANU PF ta tabbatar da shi a matsayin dantakararta a zaben shugaban kasar da ke tafe.

Da man dai rahotanni sun rawaito mai dakin shugaban, Grace Mugabe tana cewa 'yan kasar za su iya zaben 'zaben gawar mijinta'.

Kuma a baya-bayan nan ne jiga-jigan jam'iyyar ZANU PF suka sake ba wa shugaba Mugabe damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar.

A 2018 ne dai ake sa ran kasar za ta gudanar da babban zabenta, a inda kuma za a sake zaben shugaban kasa.