An yi gwanjon wayar tarhon Adolf Hitler

Wayar tarhon Adolf Hitler

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wayar tarhon mai launin ja tun daga madannan lambobi zuwa igiyarta, ta taka muhimmiyar rawa a lokacin yakin duniya na biyu

An yi gwanjon wayar tarhon da Adolf Hitler ya yi amfani da ita a lokacin yakin duniya na biyu, kan kudi dala miliyan dari biyu da hamsin a Amurka.

Sai dai ba a bayyana sunan wanda ya sayi wayar ba. An gano tarhon mai launin Ja, mai dauke da sunan shugaban Nazi a jiki, da kuma tambarin shurwa a jiki a gidansa da ke Berlin a shekarar 1945.

wadanda suka shirya bikin gwanjon kayan a birnin Maryland sun ce bayyana wayar tarhon da makami mafi daga hankali a dk cikin kayan da Hitler ya yi amfani da shi.