Ma'aikatan agaji na fuskantar cin zarafi ciki har da Fyade

Ma'aikacin agaji da wadanda ya ke agazawa
Bayanan hoto,

Ma'aikacin agaji na taimakawa

Ma'aikatan agaji na aiki a wuraren da suka fi hadari a duniya, kazalika suna fuskantar barazanar abubuwa da yawa da suka hada da harbin harsasai da bama-bamai da kuma fargabar yin garkuwa da su.

To sai dai kuma baya ga wadannan kalubale da suke fuskanta a yayin aikinsu, akwai kuma wata babbar barazana ta cin zarafinsu da ta kunno kai.

Wannan barazana da cin zarafi mata ne ke fuskantar su a yawancin lokuta.

Kimanin shekara guda da ta gabata, wata ma'aikaciyar agaji Megan Nobert ta zamo daya daga cikin wadanda suka ce an yi masu fyade.

Ita dai an yi mata fyade ne bayan da wanni abokin aikinta da suke aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ya bata wata ƙwaya da ta gusar da hankalinta.

Kuma sai ya yi amfani da wannan damar ya yi mata fyade a wannan lokaci.