Mace ta zama shugabar wani banki a Saudiyya

Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Za a kara yawan mata da ke aiki

Wani babban banki a Saudiyya ya nada mace a mastayin shugabarsa, mako guda bayan da aka nada wata mata a matsayin shugabar kasuwar hada-hadar hannayen jarin kasar.

Bankin Samba ya bayyana cewa tuni har Rania Mahmoud Nashar, ta fara aiki a ranar Lahadi.

Kwanaki uku kafin wannan nadi ne, aka nada Sarah al-Suhaimi a matsayin shugabar kasuwar hada-hadar hannayen jari a Saudiyya.

Saudiyya na kokarin kara yawan ma'aikata mata domin bunkasa tattalin arzikin kasar don magance raguwar yawan kudaden da kasar ke samu daga man fetur.

Sai dai duk da hakan, har yanzu matan Saudiyya sai sun samu cikakken izini daga mazansu ko muharraminsu kafin yin al'amura da yawa da suka hada da aiki.