Pep Guardiola: Suka za ta kashe City idan ta fadi

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Pep Guardiola ya ce yana so ya shawo kan 'yan wasan su ji dadin lokacin

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yana son 'yan wasan shi su rugunmi duk wata matsin lamba a karawar da za su yi da Monaco na wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai.

Tsohon kocin Barcelona da Bayern Munich din ya ci gasar sau biyu a matsayinshi na kociya kuma bai taba fashin kai wa wasan dab da na karshe a karo 7.

"kasancewa a nan ba abu ne mai sauki ba, "

" Ina so na shawo kan 'yan wasan su ji dadin lokacin."

Yayinda wadanda kulub biyu da Guardiola ya yi wa aiki suka zama zakarun turai sau 10 tsakaninsu.

City ta kai wasan dab da karshe a kakar bara kuma ta cigaba zuwa matakin kifa daya kwala sau hudu kawai.

" Mutane suna zato dole ne ya Manchester City ta kasance a nan amma manyan kulub da dama ba sa nan, " inji dan shekara 46. " Mu masu sa'a ne.