Ce-ce-ku-ce a Tanzania kan batun luwadi

Luwadi haramun ne a Tanzaniya kamar yadda yake a wasu kasashen Afirka da dama
Bayanan hoto,

Ce-ce-ku-ce ya barke a Tanzaniya bayan da mataimakin ministan lafiyar kasar ya yi gargadin cewar za a wallafa sunayen masu luwadi domin kama su da laifin karya doka.

A shafinsa na Twitter Mista Hamisi Kigwangalla, ya bayyana luwadi da cewa dabi'a ce ta 'yan birni, yana mai cewa babu 'yan luwadi a kauyen da ya fito na Nzega.

An dai haramta yin luwadi a Tanzaniya, kuma ana yankewa duk wanda aka kama da laifin yin hakan hukuncin daurin shekara 30 a gidan yari.

A makon da ya gabata ne gwamnatin kasar ta haramta wa wasu cibiyoyin lafiya masu zaman kansu bayar da taimakon da ya shafi cutar HIV/Aids, tana zarginsu da bai wa masu luwadi muhimmanci sosai.