Ko wane yanayi kasar Ghana take ciki?

shugaban zai yi jawabi ga 'yan kasar game da halin da take ciki
Bayanan hoto,

Shugaban kasar Ghana Nana Akuffu Addo

Shugaban Ghana ,Nana Akuffu Addo zai yi bayaki kan yanayin da kasar take ciki agaban 'yan majalasa.

Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban kasar zai sanar da al'umar kasar baki daya halin da ake ciki.

Kudin tsarin mulkin kasar ne, ya wajibawa shugaba da ya yi bayani ga 'yan kasa da zaran ya hau kan kujerar mulki, domin su san halin da ya karbi kasar a ciki.

Shugaban dai zai yi bayani ne a gaban 'yan majalasar kasar, a lokacin zaman majalasar na farko.

Bayan bayanin shugaban, 'yan majalasar kasar za su ci gaba da mahawara domin daukar matakan da suka dace , wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasar ta bangarori da dama.

Maganar ilimi da tattalin arziki da kiwon lafiya na daga cikin manyan abubuwan da za su mamaye mahawarar a zauren majalisar kasar, kamar yadda masu sharfi kan lamuren yau da kullin a kasar ta Ghana ke cewa.