Kenya ta kafa dokar yaki da fari

Fari ya addabi kasar Kenya
Bayanan hoto,

Kenya ta kadamar da dokar takadama da fari

A nahiyar Afirka, kekashewar yanayi na daya daga cikin abubuwan da ke addabar al'umma.

Shekara da shekaru da suka gabata, kasashen nahiyar da dama na gudanar da tsare-tsare, kan ta yadda za su shawo kan wannan matsala da ke hana ruwa guda ta fanin cigaba.

Gwamnatin kasar Kenya ta bayar da sanarwar kafa dokar ta-bace akan yaki da fari.

Wannan ya zo a daidai lokacin da kasashen dake makwabtaka da ita, suma na cikin wannan mawuyacin hali.

A yanzu , a maimaikon aikewa da abinci ga yankunan dake fama da yunwa, ana aika musu da kudade ta hanyoyin zamani na internet. Wannan wani sabon salo ne a gare su kuma lamari ne dake taimakawa domin rage radadin annobar da suke ciki.

Gwamnatoci da hukumar bayar da tallafi ga kasashe ta Birtaniya na rage adadin kudin aikawa da sakon, bisa yunkurin tabbatar da wadannan kudade sun kai ga wadannan yankuna.

Ga makiyaya irin wadannan kudi na tallafi na hana su sayar da dabbobinsu.Wannan kuma na taimakawa wajen bunkasa yawan dabbobin da suke da.