Kasar Congo ta yi tsayin gwaman jaki

Joseph Kabila na DR Congo
Bayanan hoto,

Shugaban kasar DR Congo Joseph Kabila

Gwamnatin kasar Dimukradiyar Congo, ta yi fatali da kiran kasashen duniya, kan gudanar da bincike game da wanni majigi da ke nuna dakarun kasar na kashe mata da maza fararen fula da basu dauke da bindiga.

Majalisar dinkin duniya dai, ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Congo da ta dubi abun da ta kira, yawaitar zargi game da take hakin bil'adama da ake cewa ya na gudana a cikin kasar.

A game da wannan lamari dai ,gwamnatin kasar Dimukradiyar Congo, ta yi mursisi game da maganar gudanar da bincike, kan wannan majigi da aka dauka a kasar.

Kakakin gwamnatin kasar ta Congo Kinshasa ko kuma dimokradiyar Congo ,ya yi tsayin gwaman jaki kan maganar binciken .Ya na nanata cewa ya rage wa wadanda suke zargin dakarun kasar ta Kongo, da aikata hakan da suka tabbatar da gaskiya kan faruwar lamarin.

Majigin da ya fito a karshen mako ,na nuna alamun an dauke shi ne, a yankin gundumar Kasai da ke tsakiyar kasar, inda sojojin kasar ta dimokradiyar Congo ke fafatawa da wasu mayakan sa kai.

Tuni dai Amurika ta yi allah wadai da faruwar lamarin da ta kira na wuce gona da iri ,game da abun da majigin ke nunawa.

Hukumar kare hakin adam ta majalisar dinkin duniya,daga bakin babban jami'in ta, Zeid Ra'ad al Hussein , ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Congo da cewa, doli ne ta duba dinbin yawan kiraye-kirayen da ake, game da zargi barkatai na yawaitar take hakin bil'adama da aka ce na gudana a cikin kasar.