Congo ta yi watsi da binciken take hakkin dan adam

Shugaba Joseph Kabila na Congo
Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da ake zargin sojojin kasar da take hakkin bil'adam ba

Gwamnatin jamhuriyar dimukradiyar Congo ta yi watsi da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi, kan a gudanar da binciken take hakkin bil'adam da sojojin kasar suka yi bayan bullowar wani hoton bidiyo da ya nuna yadda sojojin ke kashe maza da mata har da kananan yara.

Mai magana da yawun gwamnatin Congo ya ce ya rage ga wadanda ke zargin sojojin da aikata wannan laifi, su nemo shaidun da za su tabbatar da sahihancin bidiyon.

A karshen mako ne dai bidiyon ya yadu a shafukan sada zumunta, ya hasko sojojin da ke fafatawa da 'yan tawayen wata kungiyar masu dauke da makamai a yankin Kasai su na ta kashe mutane.

Tuni Amurka da sauran kasashen turai sukai Allawadai da abinda suka gani, tare da cewa matukar aka tabbatar da sahihancin bidiyon to sojin Congo sun ta ke hakkin bil'adam.

Shi ma Zeid Ra'ad al Hussein na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce dole ne gwamnatin kasar ta sake sabon lalae, da kuma bincikar zarge-zargen cin zarafin mutane da take hakkin bil'adam da aka dade ana zargin dakarun Congo da aikatawa.