Wasu kasashen Afirka za su fuskanci Fari

Mata da kananan yara sun fi shan wahala a lokacin Fari
Bayanan hoto,

UNICEF ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa, kafin abin ya munana

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya NICEF, ya ce kusan yara miliyan daya da rabi ne ke cikin hadarin kamuwa da yunwa a kasashe hudu.

Kasashen sun hada da Sudan ta Kudu, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana dokar ta bace sakamakon Fari da ya afka ma ta.

Sai kuma kasar Yemen, da Somalia sai kuma Najeriya inda ake nuna damuwa kan yiwuwar Fari sai afkawa arewacin kasar inda miliyoyin mutane ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira sakamakon rikicin Boko Haram da ya tilastawa barin muhallansu.

Yayin da yakin da ake yi a kasar Yemen ya kara yawan yaran da aka kashe iyayensu, su ke gara-ranba a sansanonin 'yan gudun hijira.

Ita kuwa kasar Somalia, wadda hasashen kwararru ya tabbata na tsadar kayan abinci da na bukatun yau da kullum suka fara bayyana, sun ce za ta sake fadawa halin da ta samu kan ta a ciki, inda a shekarar 2011 sama da mutane dubu dari biyu da hamsin suka mutu sanadiyar Fari.