"Buhari na buƙatar ya ƙara hutawa sosai"

Bukola Saraki yana ziyartar Buhari

Asalin hoton, Saraki Twitter

Bayanan hoto,

Sau biyu shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki ya kai wa Buhari ziyara a London

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce shugaba Muhammadu Buhari na bukatar karin lokaci domin ya huta sosai kamar yadda sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa suka nuna.

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Sai dai babu wani karin haske kawo yanzu da jami'an fadar suka fitar game da abin da ke damun shugaban kasar, wanda ke hutu a London.

Wasu masu sharhi a ciki da wajen kasar na kallon wannan sanarwa a matsayin wani mataki na kara kwantar da hankalin 'yan Najeriya.

Shugaban Najeriyar dai ya bar kasar a ranar 19 ga watan Janairu domin fara hutu a Burtaniya, inda kuma aka ce za a duba lafiyarsa.

Sai bai dawo kamar yadda ya ce ba a ranar 6 ga watan Fabrairu, amma ya bukaci karin wutu domin a karasa masa wasu gwaje-gwaje game da lafiyarsa.

Kafin tafiyar tasa dai shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar ga matainakinsa, farfesa Yemi Osinbajo.

Sai dai tsawaita hutun nasa da kuma rashin bayyana takamaimai abin da ke damun shugaban kasar ya janyo kace-nace a cikin kasar., har ma wasu suka dinga yada jita-jitar cewa ya mutu.

Hakan ce ta sa wasu masoyansa suk dinga fitar da hotunansa da ya dauka da wadanda ke kai masa ziyara a London din, don su nuna cewa yana nan da ransa.

Masoyan shugaban da dama sun yi ta masa addu'o'i a masallatai da coci-coci, suna fatan ya samu sauki ya kuma dawo don ci gaba da mulkinsa lafiya.