Ruwa ya koro gawawwakin 'yan ci rani 87 bakin tekun Libya

An ga gawawwakin da ruwa ya koro birjik a bakin teku
Bayanan hoto,

An ga gawawwakin da ruwa ya koro birjik a bakin teku

Kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent da ke Libya, ta ce ta gano gawawwakin 'yan ci rani 87 a gabar teku a kusa da garin Zawiya da ke Yammacin kasar.

Kungiyar ta kuma ce akwai ragowar gawarwaki da dama a cikin tekun.

Jami'ai sun yi ammanna cewa wadanda abin ya rutsa da su suna cikin jiragen ruwa guda biyu ne da suka nufi gabashin kasar daga yankunan da ke tsakanin Zawiya da Mellitah a karshen makon da ya gabata.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta Red Cross da Red Crescent da ke lardin, Steven Ryan, ya ce akasarin 'yan ci ranin sun yi balaguro mai cike da hadari kafin isa Libya, inda daga nan kuma suke sake shiga wani hadarin da ke tattare da tsallaka tekun Bahar Rum.

Ya ce, "Har yanzu wannan ce dama daya da mutane ke da ita ta shiga Turai. A bara war haka mun ga mutane masu tarin yawa da ke tafiya daga Turkiya zuwa Girka, daga nan kuma su shiga wasu kasashen Turai."

A kalla 'yan ci rani 5,000 ne suka nutse a lokacin da suke kokarin ketare tekun Bahar-rum zuwa nahiyar Turai a shekarar 2016.