Ba zan yafa mayafi don ganawa da malami ba — Le Pen

Marine Le Pen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Marine Le Pen tana adawa da bai wa 'yan gudun hijira mafaka a Faransa

'Yar takarar shugabancin kasar Faransa mai adawa da 'yan gudun hijira, Marine Le Pen, ta soke wata ganawa da za ta yi da babban Malamin addinin Musulunci na kasar Lebanon, bayan ta ki yafa mayafi kamar yadda ya bukace ta.

Ta ce ba ta ga dalilin da zai sa ta yafa mayafi don rufe kanta ba saboda ganawar da malamin, ganin cewa Babban Muhutin Al'azhar ma, wanda shi ne malami mafi karfin fada aji na Sunnah a duniya, bai bukaci hakan ba lokacin da ta gana da shi a Alkahira.

Ms Le Pen ta shaida wa manema labarai da jami'ai a wajen ofishin babban malamin cewa, "Na gana da babban malamin addinin musulunci na Al Azhar, bai bukaci na yi hakan ba. Ba wani abin tashin hankali ba ne, za ku iya sanar da shi abin da na fada."

Kashin bayan kamfe dinta dai shi ne, adawar da ta ke nunawa kan abin da ta kira kakaba dabi'un Musulunci a kan al'adun Faransa.