Birtaniya ta hana masu karamin karfi kai iyalansu kasar

Silhouette of a split family

Asalin hoton, Thinkstock

Kotun Kolin Birtaniya ta tabbatar wa gwamnati hakkin kayyade mafi karancin albashin da 'yan kasa za su rika karba, kafin a kyale su su shigar da mazaje ko matansu kasar.

Kotun kolin ta ce hakan bai sabawa dokar danne hakki ba.

Alkalan kotun sun ce dokar kariya ce ga wadanda abin ya shafa, saboda kudin da suke samu ba zai ishe su su dauki nauyin kansu da iyalan nasu ba idan har suka mayar da su Birtaniyan.

A shekarar 2012 ne gwamnatin kasar ta sa dokar cewa dole duk wasu 'yan Birtaniya masu mazaje ko mataye da suke wasu kasashen, ya kasance kudin da suke samu ya kai fam 18,600, kafin iyalansu su koma Birtaniyan da zama tare da su.

Masu sukar lamiri sun yi korafin cewa kusan yara 15,000 ne aka raba su da iyayensu sakamakon wannan doka.

Nasarar da gwamnatin ta samu a wannan shari'a na nufin cewa dubban ma'aurata a Birtaniyan za su ci gaba da zama ba tare da iyalansu ba.

A wasu gwaje-gwaje da aka yi, wasu ma'auratan da abin ya shafa sun yi korafin cewa dokar ta take hakkinsu na zamantakewar iyali.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Biyu daga cikin wadanda suka yi wannan korafin, Abdul Majid and Shabana Javed, 'yan asalin Birtaniya ne wadanda abokan zamansu kuma 'yan Pakistan ne.

Akwai kuma wani dan gudun hijirar Labanon wanda ya kasa samun aiki a Birtaniya, duk da cewa yana da cikakkun takardun kammala karatun digiri dinsa na biyu.

Ya ce matarsa ma tana da ilimi mai zurfi kuma tana jin Turanci sosai.

Shari'a ta karshe da aka yi kan wannan lamari ta shafi wani dan gudun hijirar Congo ne da Birtaniya ta ba shi cikakken izinin zama amma matarsa ba ta samu izinin zama tare da shi ba.

'Ban taba haduwa da dana ba'

Wata mata da abin ya shafa Laura Clarke, daga Rugby a Warwickshire, wadda take aiki a kasar Habasha a lokacin da ta hadu da abokin zamanta, amma ta koma Ingila da zama inda ta haifi dansu na farko.

Ta shaida wa BBC cewa mijin nata ba zai iya zuwa Birtaniya su zauna tare ba, saboda ba ta da karfin da za ta iya daukar dawainiyarsa.

"Ba zai iya kawo mana ziyara ba an hana shi bizar zuwa ziyara ma, saboda dalilin cewa ya taba zuwa kuma tun da yana da iyali a nan ba lallai ne in ya zo ya koma ba," inji ta.

Ta kara da cewa, "Ina jin tausayin dana, don bai taba ganin mahaifinsa ba."

'Dogaro da gwamnati'

Tsohuwar gwamnatin hadaka ce ta sanya wannan doka saboda a hana ma'auratan da ba 'yan kasar ba dogaro da aljihun gwamnati.

Batun albashi mafi karanci da mutum yake fara samu, wanda ya shafi mutanen da ke zaune a Birtaniya a matsayin 'yan gudun hijira, zai karu zuwa fam 22,000 idan ma'aurata na da yaran da ba su da shaidar zama 'yan kasar Birtaniya, da kuma karin fam 2,400 a kan sauran yaran baya ga na farkon.

A shekarar 2013 ne, babbar kotun kasar ta yanke hukunci da ya yi wa ma'auratan dadi, inda ta ce waccar dokar ba ta yi musu adalci ba.

A lokacin da gwamnati ta dauki wannan mataki, ta ce ta yi hakan ne saboda ta rage dogaron da ake yi a kanta, da kuma yadda ake amfani da wannan damar wajen turuwar iyalai 'yan gudun hijira zuwa Birtaniya.

Masu fafutuka sun ce kusan rabin 'yan Birtaniya za su ji jiki da wannan doka, saboda masu karamin karfi ne, inda hakan ke nufin ba su ba zama tare da iyalansu.