Kotu ta hana Afirka ta Kudu ficewa daga ICC

South Africa
Bayanan hoto,

Kasashen Afirka da dama na son ficewa daga IC

Wata kotu a Africa ta Kudu ta hana gwamnatin kasar yunkurinta na janyewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC.

Babbar kotun ta ce gwamnatin kasar bata bi ka'idar tsarin mulki ba, saboda kamata ya yi gwamnati ta fara samun amincewar majalisu.

Mataimakin babban alkalin toun, Mojapelo ne ya karanto shawarar da kotun ta yanke.

Ya ce, "A tun farko ba a bi tsarin kundin mulki ba wajen bayar da sanarwar janyewa daga kotun ta ICC, wadda ministan huldar kasashen waje ya sanaywa hannu a ranar 19 ga watan Oktoba."

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, ministan shari'ar kasar Michael Masutha ya mayar da martani cewa har yanzu gwamnatin tana kan aniyarta ta ficewa daga ICC.

Ya ce, "Gwamnati za ta duba zabin da take da shi da ya hada da yiwuwar daukaka kara, bayan ta yi nazarin gaba daya shari'ar.

Wakilin BBC da ke Johannesburg, ya ce hukuncin wani nasara ne ga jam'iyyar adawar Afirka ta Kudun, wadda ta sha kalubalantar jam'iyya mai mulki ta ANC a kotun.

Kasar Afirka ta Kudu na daya daga cikin kasashen da suka sanar da shirin ficewa daga kotun ICC.