Farmajo ya sha rantsuwar mulkin Somaliya

Farmajo

Asalin hoton, Twitter Farmajo

Sabon shugaban Somaliya, Mohamed Abdullahi Farmajo, ya sha rantsuwar karbar mulki tare da yin jawabi a Mogadishu babban birnin kasar.

Ya yi alkjawarin inganta tsaro da kuma aiki domin samar da sulhu a kasar.

Shugabannin yankin kasashen Gabashin Afirka, wandanda suka hada da na Kenya da Habasha sun halarci bikin rantsuwar.

'Yan majalisar Somaliya ne suka zabi shugaba Farmajo makonni biyu da suka gabata, inda ya kada shugaba mai barin gado Hassan Sheikh Mohamud.

A jawabin nasa, shugaba Farmajo ya gargadi masu tayar da kayar baya na Al Shabab cewa ba za su iya fin karfin 'yan Somaliya miliyan 12 ba.

A lokacin da ya ke jawabi a wurin taron, Firai ministan Habasha, Hailemariam Desalegn, ya bayar da goyon bayansa ga sabon shugaban Somaliyar.

Ya ce, "Mutanen Somaliya sun baka goyon baya dari bisa dari domin ka samar da kwanciyar hankali da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Ina fatan ba za ka basu kunya ba saboda zaben ka da suka yi, a matsayin wanda suke sa ran zai farfado da Somaliya.

Masu sharhi sun ce sabuwar gwamnatin zata fuskanci manyan kalubale a yayin da yake yakar ta'adancin kungiyar Al Shabaab, da matsanancin fari wanda yasa kasar ta samu kanta a cikin bala'in yunwa.

Wane ne sabon shugaban Somaliya?

A wani sharhi da jaridar Buffalo Times ta Amurka ta wallafa kan ko wane ne sabon shugaban Somaliya, ta ce mutum ne mai kazar-kazar a cikin al'ummarsa a lokacin da yake zaune a birnin New York.

Mista Mohammed yana da shaidar zama dan Somaliya da kuma Amurka, kuma shekara biyu da ta gabata ne ya koma Somaliya don tsayawa takara.

Jaridar ta yi hira da mutanen da suka san shi, wadanda suka ce yana da kwarjini da dattako, wanda ke yin kyakkyawar mu'amala da 'yan gudun hijira da manyan 'yan siyasa da fitattun 'yan wasan kwallo.

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da ya yi a rayuwarsa:

A shekarar 1985 ne Mista Mohammed ya koma Amurka

A shekarar 1993 kuma ya samu kammala digirinsa a fannin Tarihi a jami'ar Buffalo

A shekarar 2009 ne ya kammala digirinsa na biyu a fannin nazarin al'amuran da suka shafi Amurka.

Yana daga cikin mambobin jam'iyyar Republican kuma ya taka rawa a yakin neman zabe da dama

Yana da 'ya'ya hudu.

'Yarsa mai shekara 24 ta ce, mahaifin nata ya samu lakanin 'Farmajo' ne daga sunan chukwi a yaren Italiya, daga wajen mahaifinsa, saboda son da yake wa abincin kasar Italiya.

Shi ne ya kirkiro da wani shiri na horar da 'yan gudun hijirar Somaliya da ke Amurka harkokin kananan kasuwanci.