Masana falaƙi sun ce sun gano wasu duniyoyi

Duniya

Asalin hoton, Eso

Bayanan hoto,

Mai yiwuwa za a iya samun ruwa a cikin wasu daga cikin duniyoyin

Masana falaƙi sun ce sun gano wasu duniyoyi da ke kewaya wani tauraro mai nisa, wanda kuma ke da yanayin da za iya rayuwa a cikinsa.

Masanan, wadanda suka fito daga kasashe daban-daban, ciki har da Amurka da Burtaniya da Belgium, sun ce sun gano duniyoyin bakwai ne, wadanda kowace girmanta ya kai duniyar da muke ciki, suna kewaya wani tauraro mai suna Trappist-1.

An yi amannar cewa nisan duniyoyin daga tauraron ya yi daidai da yadda za a iya samun ruwa a cikinsu.

Masana kimiyya na fatan samun damar yin cikakken nazari a kan duniyoyin nan gaba, ta hanyar amfani da na'urorin hangen nesa.

Amma za a iya daukar daruruwan shekaru kafin mutane daga wannan duniyar tamu su iya zuwa can.