Buhari ya yi magana da jama'ar Kano
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Buhari ya yi magana da gwamnan Kano ta wayar tarho

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magana da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta wayar tarho a daidai lokacin da ake yin taron yi masa addu'o'in samun sauki a gidan gwamnatin jihar ta Kano.

Shugaban kasar, wanda ya kwashe fiye da wata guda ba ya kasar, ya gode wa 'yan Najeriya bisa addu'o'in da suke yi masa.

Gwamnan na Kano ya yi masa fatan samun sauki, yana mai mika fatan alherin 'yan jihar a gare shi.

Labarai masu alaka