Nigeria: An sace Jamusawa biyu a Kaduna

Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda sun ce za su yi kokarin ganin an ceto mutanen lafiya lau
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce wasu 'yan bindiga sun sace wadansu Jamusawa biyu a jihar Kaduna da ke Arewacin kasar.
Wani mai magana da yawun 'yan sandan kasar ya ce an sace mutanen ne da safiyar ranar Laraba.
Rundunar 'yan sandan ta ce Jamusawan na daga cikin tawagar masu binciken ma'adinan kasa a kauyen Jajela a karamar hukumar Kagarko da ke jihar.
Ta kara da cewa 'yan bindigar basu nemi a biya su kudin fansa ba kafin su sako mutanen. Amma ta ce jami'an tsaro na kokarin gano su.
Rahotonni sun ce wadanda aka sacen sun zo ne daga jami'ar Goethe da ke birnin Frankfurt a kasar Jamus.
Har yanzu dai ma'aikatar harkokin wajen Jamus bata ce komai ba a kan lamarin.
Garkuwa da mutane a Najeriya don neman kudin fansa ya zama ruwan dare, a kasar da ke fama da matsalolin tattalin arziki mafi muni a 'yan shekarun nan.
A baya-bayan nan ne jihar Lagos ta kaddamar ta hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da irin wannan laifin.