Kamaru ta kori 'yan gudun hijirar Nigeria 517

Dubban 'yan gudun hijira ke samun mafaka a Kamaru
Bayanan hoto,

Dubban 'yan gudun hijira ke samun mafaka a Kamaru

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, ta ce Kamaru ta kori 'yan gudun hijirar Najeriya 517, da kuma masu neman mafaka 313, wadanda suka koma kasar sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

UNHCR ta nuna damuwarta a kan hakan tare da yin kira ga Kamaru da ta bai wa 'yan gudun hijirar mafaka, tare da girmama yarjejeniyar kasashen duniya ta gujewa korar masu neman mafaka.

Hukumar ta ce akwai shirin da take yi na kulla yarjejeniya tsakanin Najeriya da Kamaru ranar biyu ga watan Maris, don mayar da 'yan gudun hijirar Najeriya 85,000 a bisa tsari.

Dama ko a watan Yunin 2016 ma Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da UNHCR, da kuma jamhuriyar Kamaru, kan mayar da wasu 'yan gudun hijirarta cikin aminci da suke samun mafaka a Kamaru.

Rahotanni sun ce irin wannan rikicin ya faru a Gabashin Afrika a baya-bayan nan, inda gwamnatin Kenya ta yi yunkurin rufe sansanin 'yan gudun hijirar Somaliya, wanda shi ne mafi girma a duniya.

Ko a watan Disambar 2015 ma, hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa Kamarun ta taso keyar 'yan Najeriya fiye da 18,000 zuwa kasarsu.

Hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ya kuma raba dubun dubatar mutane da muhallansu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Da yawan mutanen suna gudun hijira a wasu jihohin a kasarsu, yayin da wasu kuma suka tafi makwabtan kasashe irin su Kamaru da Chadi don neman mafaka.