'Dogon bacci ga manya alama ce ta cutar mantuwa'

Yawanci an fi samun cutar Alzheimers ga tsofaffi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yawanci an fi samun cutar Alzheimers ga tsofaffi

Wani sabon bincike ya nuna cewa manyan mutanen da suka fara sharar barci fiye da tsawon sa'a tara a ko wanne dare -- duk da yake a baya ba sa yin hakan -- mai yiwuwa suna dauke da alamun farko-farko na cutar Alzheimers mai gigita hankali da sa yawan mantuwa.

Wani nazarin da aka yi sama da shekara 60, ya gano cewa mutanen da ke dankarar barci fiye da tsawon sa'a tara, na da ribi biyu na yiwuwar kamuwa da cutar mai sa gigi.

Masu binciken a jami'ar Boston ta Amurka, sun ce tambayar mutane tsawon sa'a nawa suke barci, na iya zama abu mai matukar amfani wajen gano wadanda ke cikin karuwar hatsarin daukar cutar mantuwa.

Dakta Matthew Pase, wanda ya jagoranci binciken, ya bayyana cewa akwai yiwuwar samun alaka tsakanin bacci mai tsayi da cutar mantuwa.