India: Dan siyasa ya bai wa wurin bauta kudin gwamnati

Mafi yawan al'ummar Indiya mabiya addinin Hindu ne

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mafi yawan al'ummar Indiya mabiya addinin Hindu ne

An soki lamirin wani dan siyasar kasar Indiya, bayan da ya kashe dala 750 na kudin gwamnati wajen sayen gwala-gwalan da ya bayar sadaka ga wani wurin bauta.

Chandrashekkhar Rao ya bayar da sadakar ne ga wani fitaccen wajen bautar addinin Hindu mai suna Tirumala, saboda nuna farin ciki da kirkiro wata sabuwar jiha mai suna Telengana a kasar ta Indiay, jihar da shi ne ke shugabantarta.

Wannan ba shi ne karon farko da aka zarge shi da yin bushasha da dukiyar jama'a ba.

'Yan jam'iyyun adawa a jihar Telengana sun ce kamata ya yi Mista Rao ya fi sanin hanyar da tafi dacewa ya kashe kudin jama'a, amma ba a irin hanyar neman birgewa ko riya ba.

Ya yi hakan ne yayin da fada-fada na wajen bautar suke sowa, inda ya lankaya dankareriyar sarkar zinarin a wuyan abin bautar da kuma kyautar furanni.

A watan Oktobar 2016 ma ya yi irin wannan kyautar bajintar ta zinare mai tsada a wajen wani abin bautar, jim kadan kuma sai ya sake bayar da sadakar gashin baki na danyen zinare.

Duk da yake dai masu sharhi suna cewa Mista Rao yana gudanar da ayyuka ne na kyautata addininsa, to amma fa yana yi ne da kudin al'umma.

A baya-bayan nan ma an soke shi saboda mallakar wani gida na kece-raini, wanda yake da badakuna gagara harsashi.