Girgizar kasa ta afkawa kogin Tangayinka a Tanzania

Kogin Tangayinka ne mafi zurfi a Afirka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kogin Tangayinka ne mafi zurfi a Afirka

A ranar Juma'a da safe ne aka samu girgizar kasa mai girman maki 5.7 a kogin Tangayinka, wanda shi ne na biyu mafi zurfi kuma na biyu mafi girma a Afirka.

Tasirin girgizar kasar ya fi shafar garin Kapula ne da ke yammacin Zambiya, wanda ke kan iyakar Tanzaniya Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo.

Babu wani rahoto na mutuwa ko jin rauni, duk da cewa wani ganau ya ce mazauna yankin kudu maso gabashin Tanzaniya sun shiga cikin fargaba.

A watan Satumbar shekarar da ta gabata ma , an yi wata girgizar kasa mai karfin gaske a arewa maso yammacin Tanzaniyan, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 16, da kuma jawo dumbin asarar ababen more rayuwa a yankin.

Wani shafin intanet da yake lura da yanayin al'amuran da suke shafi girgizar kasa, ya yada wani hoton bidiyo na wuraren da abin ya shafa.