'Yan Afirka ta Kudu da 'yan ci rani sun yi fito-na-fito

'Yan sanda sun yi kokarin hana taho-mu-gama tsakanin bangarorin biyu

Asalin hoton, Sofia moreira Twitter

Bayanan hoto,

'Yan sanda sun yi kokarin hana taho-mu-gama tsakanin bangarorin biyu

'Yan sanda a Afirka ta Kudu sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye da harsashin roba domin tarwatsa daruruwan 'yan kasar da baki 'yan ci rani, wadanda ke maci a Pretoria babban birnin kasar, sakamakon wawushe shagunan 'yan ci rani da aka yi a farkon makon nan.

'Yan kasar da baki 'yan ci ranin sun yi fito-na-fito a birni, amma sai 'yan sanda suka shiga tsakaninsu.

'Yan sandan sun yi amfani da dabaru da suka hada da amfani da jirgi mai saukar ungulu don ganin bangarorin biyu ba su tunkari juna da nufin kece-raini ba.

Wasu masu macin da dama sun je ofishin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar domin gabatar da wata takardar korafi.

'Yan kasar dai na adawa ne da zaman baki 'yan ci rani saboda a ganinsu suna toshe musu damar samun ayyukan yi a kamfanonin kasar.

Hakan ya sa su ke yawan kai musu hare-haren kin jinin baki kan shagunansu da sauran wuraren sana'arsu.

Su kuwa 'yan ci rani sun fito ne don nuna rashin goyon bayansu ga abin da 'yan kasar ke musu.

Ko wanne bangare ya ja daga don nuna jajircewa kan al'amarin.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter, wani mutum dan ci rani ya ce ba sa son yin fada, "amma a shirye mu ke mu kare dukiyoyinmu."

Dukkan bangarorin biyu suna dauke da sanduna da duwatsu da kuma wukake.

Bayanan hoto,

Magajin garin birnin Johannesburg Herman Mashaba, ya yi tir da hare-haren

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugaba Jacob Zuma na kasar ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankalinsu su kuma zauna lafiya.

Ya yi Allah-wadai da kai hare-hare da matsawa 'yan ci ranin wasu kasashen Afirka mazauna kasar da ake yi.

A wata sanarwa da ya fitar ya ce, zai yi iyawarsa don ganin ya kawo karshen munanan laifuka da kuma kawo zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al'ummomin kasar.

A farkon makon nan ne, wasu bata-gari 'yan Afirka ta Kudu suka far wa shagunan 'yan Somaliya da Pakistan da ma 'yan wasu kasashen a birnin Pretoria da Johannesburg.

Cikin wadanda hare-haren ke shafa har da dumbin 'yan Najeriya da ke zaune a can.

Amma 'yan ci ranin Najeriyar sun yi watsi da zargin da ake musu na karuwanci da safarar miyagun kwayoyi.

Mista Zuma ya kuma yi tir da yadda ake kara rura wutar kin jinin baki a kafafen sada zumunta na zamani.

A ranar Alhamis ma wasu matasa 'yan Najeriya sun yi zanga-zanga a kofar ofishin kamfanin wayar sadarwa na MTN mallakin Afirka ta Kudu, inda suka farfasa gilasan ofishin tare da balla allunan tallar kamfanin.

Masu sharhi dai na ganin dole Afirka ta Kudu ta zauna da kasashen da abin ke shafar mutanensu, don kawo karshen wannan lamari.

A ganinsu hakan ne kawai zai hana tabarbarewar al'amura da lalacewat dangantakar da ke tsakanin kasashen, musamman ma da Najeriya, inda kamfanonin Aforka ta Kudun da dama suke huldar kasuwanci sosai a can.