Nigeria: Dala ta fara sauka a kasuwar bayan fage

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tashin dala ya sa al'ummar Najeriya cikin halin ha'ula'i saboda yadda farashin kayayyaki suka tashi

Farashin dala ya fadi sosai a karon farko a kasuwannin bayan fage na NAjeriya, kasa da mako guda bayan da babban bankin kasar CBN, ya bayyana matakin bunkasa samar da ita ga masu nema a bankuna.

Matsalar karancin dala a bankunan Najeriya wanda sakamakon rashin wadatar kudaden kasashen wajen a CBN, ya sa dalar ta yi ta tashin gwauron zabi, a kasuwannin bayan fage na kasar.

Wasu na ganin wannan ne dalilin da ya sa kayayyakiin masarufi da na amfanin yau da kullum suke kara hauhauwa, duba da cewa kasar ba ta faye fitar da kaya zuwa wasu kasashe ba.

Kazalika kudaden kasashen wajen da take samu ya ragu sakamakon rage sayen man fetur dinta da Amurka ta yi, da kuma janyewar masu zuba jari.

Wakilin BBC ya ziyarci kasuwar musayar kudi ta WAPA da ke Kano a arewa maso gabashin Najeriyar, inda ya tattauna da wasu 'yan kasuwar kan farashin dala., inda ya ji ta bakin 'yan kasuwar.

Sani Salisu Dada ya shaida wa BBC cewa, "A cikin 'yan kwanakin nan kullum kara sauka dalar take yi ba kamar baya ba da kullum sai dai farashinta ya yi sama."

Me yasa dalar take sauka?

Malam Sani ya ce hakan ba zai rasa nasaba da sanarwa da gwamnati ta yi ba na cewa CBN za ta kara yawan dalar da take bai wa bankuna.

"Kuma ka ga ba a bata l;okaci ba wajen fara ba su, don yau Alhamis ma naje banki kuma naga wani ya karba, matafiyi ne kuma an sayar masa da ita a kan naira 375 duk dala daya, bayan kuwa da safe ana sayar da ita a nan kasuwa 505, inji shi.

Ya kara da cewa, "Amma yanzu kuma maganar da nake da yamman nan, ganin bankuna suna bayarwa, yanzu a kasuwa ta dawo 470 zuwa 475."

Wasu rahotannin ma sun ce a makon da ya gabata sai da aka sayar da duk dala daya a kan naira 516.

'Yan kasuwar sun ce in abin ya dore, to farashin zai iya dawowa daidai a bankuna da kasuwar bayan fage.

'Yan kasuwar dai sun ce fatansu shi ne dalar ta yi ta sauka domin a samu saukin rayuwa.

Ga dai yadda cikakkiyar hirar tasu da Yusuf Ibrahim Yakasai ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Dala ta sauko a kasuwar bayan fagen Nigeria

Shi ma wani masanin tattalin arziki a Najeriyar Abubakar Aliyu, ya ce abin bai zo da mamaki ba, kuma idan har matakin bankin ya dore to lallai za a samu sauki sosai.

"Ko a yau Juma'a ma dalar ta sake sauko zuwa naira 390 a kasuwar bayan fage," inji shi.

Ya kara da cewa ana hasashen za ta sauko har zuwa naira 350 kan ko wacce dala daya.

"Saboda haka gara ma duk wanda ya san ya boye dala don idan ta yi tsada ya sayar, to a fito da ita yanzu tun kafin ta zame wa mutane asara," a cewar Mista Aliyu.

A ranar Litinin ne CBN ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.

CBN ya fitar da sabbin manufofin kudin kasashen waje

A karkashin sabon tsarin, Babban Bankin ya ce zai kara yawan kudaden wajen da ya ke bai wa bankunan kasar da nufin saukakawa 'yan Najeriya masu bukatar zuwa asibiti a wasu kasashen, da masu karatu a wasu kasashen da kuma 'yan kasuwa.

Labarai masu alaka