'Yawan cin kayan marmari na iya kawo tsawon rai'

'Ya'ya itatuwa da kayan lambu

Asalin hoton, iStock

Bayanan hoto,

'Ya'yan itatuwa da kayan lambu na kawo tsawon rai

Masu bincike sun bayyana cewa yawan cin kayan marmari da ganyayyaki a ko wacce rana na iya sa tsawon rai.

A wani binciken da kwalejin Imperial ta Biritaniya ta gudanar, ya nuna cewa irin wannan kayan abinci za su iya kare mutane milliyan 7.8 daga mutuwa sanadin kananan cututtuka a ko wace shekara.

The team also identified specific fruit and veg that reduced the risk of cancer and heart disease.

Masanan sun kuma gano wasu kayan marmari da ganyayyaki na musamman da ka iya rage hadarin kamuwa da ciwon daji ko cancer da cututtukan da suka shafi zuciya.

Binciken ya ce ko da cin kayan marmari da ganyayyakin kadan ma na kara lafiyar jiki amma cin su da yawa yafi amfani.

Kayan marmarin ko ganyayyakin kamar nauyin giram 80 - daidai yake da karamar ayaba ko fiya ko babban cokali uku na alayyahu ko kuma waken Bature.

A karshe dai an tattaro bayanai daga bincike 95 da aka yi daban, wanda suka yi duba a kan halayyar cin abinci ta mutane miliyan biyu.

Za'a rage hadarin kamuwa da ciwon cancer idan ana ci:

  • Korayen ganyayyaki (kamar alayyahu)
  • Kayan lambu mai launin dorawa wato yellow, (kamar tattasai mai wannan launi)
  • Kayan lambu dangin kabeji

Za'a rage hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da shanyewar jiki idan aka ci:

  • Tuffa
  • Fiya
  • 'Ya'yan itatuwa dangin lemo
  • kwadon ganyayyaki
  • Kayan lambu masu koren ganye (kamar Latas)
  • Kayan lambu dangin kabeji
Bayanan hoto,

Harriet na cin alayyahu da yawa

Harriet Micallef, daga Chippenham, tana yawan cin kayan marmari kamar sau takwas a ko wace rana, tana kuma yawan cin abincin mai dauke da alayyahu sosai.

Harriet ta shaidawa BBC cewa "Ina cin su sosai, ban taba cin wani abinci, ba tare da 'ya'yan itatuwa ko hadin ganyayyaki ba a kullum."

Harriet ta kara da cewa tana cin kwai da aka sawa kayan lambu da alayyafu, wasu lokutan kuma ta sa masa fiya ko tumatiri.

Bayanan hoto,

'Ya'yan itatuwa da kayan lambu na rage hadarin kamuwa da wasu cututuka

Masu binciken ba su san ko cin kayan marmari da na lambu da yawa sosai na iya kara inganta lafiya tun da ba a samu wasu bkwararan hujjoji ba kan hakan.

Daya daga cikin masanan, Dr Dagfinn Aune, ya ce: "'Ya'yan itatuwa da kayan lambu na iya rage kitsen jiki da hawan jini, da kara lafiyar jini da kuma rigakafin kamuwa da cututtuka.

Wannan na iya zama saboda sanadaran gina jiki da suka kunsa''.

"Suna kunshe da wasu sinadaran da ke iya rage lahani ga kwayoyin haliyar dan adam, wanda zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon daji."

Duk da haka, da kyar wasu mutanen ke iya cin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu giram 400 a rana, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayar da shawara.

A Birtaniya, mutane daya daga cikin uku ke cin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu da yawa.

Bayanan hoto,

Heather na son cin dankali

Heather Saunders, mai shekeru 24 daga Oxford, tana cin 'ya'yan itatuwa da kayan lambu awo tara ko goma a kowace rana tun da ta daina cin nama.

Ta na cin 'ya'yan itace biyu a yayin karin kumallon safe, ta kuma ci kayan lambu mai yawa lokacin cin abincin rana, sa'annan ta ci a kalla kayan lambu hudu da yamma.

Heather ta shaidawa BBC cewa, "Ni na yake shawara, kuma ina ganin cin 'ya'yan itace da kayan lambu ya fi lafiya."