BH: Za a tara $670m don tallafawa yankin tafkin Chadi

Nigerian Refugee

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban mutane ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira a Arewa maso gabashin Najeriya.

Kasashen duniya sun sha alwashin tara dala miliyan 670 don taimakon gaggawa ga mutanen da ke fuskanatar barazanar fari a yankin tafkin Chadi da ke Yammacin Afirka.

Yankin wanda ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi ya sha fama da rikice-rikice da tabarbarewar al'amura sakamokon hare-haren kungiyar Boko Haram.

Za a dauki shekara uku ana tara kudin.

An sanar da hakan ne a wani babban taro da aka fara a Oslo babban birnin kasar Norway, domin tara kudade cikin gaggawa don taimaka wa miliyoyin mutane da ke cikin halin ha'ula'i a yankin.

Ministan harkokin wajen Norway, Borge Brende, ya ce tarzomar na daya daga cikin rikice-rikice da duniya ta fi nuna halin ko in kula da su.

Ya ce, "Wannan taro ya bamu dama a matsayinmu na kasa, mu jawo hankalin duniya a kan irin kokarin da gwamnatin Najeriya da sauran abokan hulda ke yi wajen magance babbar matsalar da ke kara bayyana a Arewa maso Gabashin Najeriya.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fiye da 'yan gudun hijira 16, 000 ne ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira na wucen gadi a wajen Maiduguri.

Sharhi: Sadiya Umar Farouk:

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Najeriya, Sadiya Umar Farouk, ta ce hukumar tana fatan cewar za a samu iya gudumawar da ake so domin agaza wa 'yan gudun hijira.

Ta kara da cewa hukumar na da kyakkyawan fatan cewa in aka samu kudin za a yi aiki da su ta hannyara da ta dace.

Har wa yau ta ce bukatun da Najeriya ta gabatar a taron sun hada da maganar mayar da 'yan gudun hijirar muhallansu, da samar da asibitoci, da kuma mayar da miliyoyin yara makaranta.

Rikicin Boko haram ya hana manoma noma ko samun damar kai dabobbinsu mashaya.

Masana sun ce rikicin ya kuma hana masu kamun kifi damar zuwa tafkin da kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da kuma Chadi ke amfani da shi.

Rikice-rikicen kungiyar boko Haram sun yi mummunar illa ga yankin, da dama can yake daya daga cikin wadanda ke fuskantar talauci a duniya, sakamakon shekara takwas na rikici da ya ke fuskanta.

A lokacin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai, Ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama ya ce gwamntin kasar na fatan yin aiki da abokan huldarsu na kasashen duniya domin shawo kan rikicin.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Dubban 'yan gudun hijira ne ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijiran da ke Maiduguri

"A matsayinmu na kasa, wannan taron ya bamu damar jawo hankali a kan irin kokarin da gwamnatin Najeriya da abokan huldarmu ke yi kan magance matsalolin da ke tasowa a yankin, kuma a karfafa anniyarmu da hadin gwiwa daku wajen shawo kan gagarumin kalubalen da muke fuskanta," inji ministan.

Jami'ai sun ce duk da cewa an kori 'yan Boko Haram daga yankunan da ke karkashin ikonsu a shekarar 2014, hare-harensu da yakin da hukumomin tsaron Najeriya ke yi da su, na shafar muhimman ayyukan tattalin arzikin kasar.

Kungiyar Boko Haram ta yi sanadin mutuwar a kalla mutane kusan 15,000, tare da tilastawa sama da miliyan biyu barin muhallansu a cikin shekaru bakwai na rikicin.

Yayin da ake wannan kuma, su ma shuwagabannin kasashen Sudan ta Kudu da Habasha wato Ethiopia, sun roki kasashen duniya da su taimaka wa miliyoyin mutane da ke fuskantar barazanar yunwa a wasu sassa na Sudan ta Kudun, yayin da ita kuma Ethiopia ke fama da fari.

Sun yi kiran ne bayan da suka gana a birnin Addis Ababa na Ethiopian.