Gizo ya narkawa yaro mumman dafi sakamakon cizo

Spider

Asalin hoton, Australian Reptile Park

Bayanan hoto,

Irin wannan gizon na cikin wadanda suka fi hatsari a duniya

Rahotanni daga Australiya sun ce wani yaro dan shekara 10 ya tsallake rijiya da baya, bayan da wani gizo-gizo da ke da mummunan dafi ya harbe.

Al'amarin ya sa sai da aka bai wa yaron maganin kashe dafi har kwalba 12.

Ana ganin wannan shi ne maganin kashe dafi mafi yawa da aka taba bai wa wani majinyaci a kasar Australiya.

Gizon ya harbi Matthew Mitchell ne a yatsa, yayin da yake taya mahaifinsa share shago.

Ya yi ta yanke jiki yana faduwa, kwayoyin idanunsa sun fito sosai har kumfa ta fara fita a bakinsa.

Yaron ya shaida wa jaridar kasar mai suna Daily Telegraph cewar:"Gizon ya manne a yatsata, kuma na kasa cire shi."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A watannin Fabrairu da Maris ne irin wannan gizon suka fi haihuwa.

Iyayen Matthew sun yi amfani da riga wajen hana dafin yaduwa a jikinsa a lokacin da suka garzaya da shi asibiti.

An kama gizon kuma an kai shi wani gidan ajiye namun daji da ke kusa da Sydney inda ake tatsar dafinsa.

Manajan gidan adana namun dajin, Tim Faulkner, ya ce, 'Mathew ya taki sa'a da bai mutu ba.'