Man U za ta kara da FC Rostov a gasar Europa League

Manchester United

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Manchester United tana fatan isa wasan karshen da za a buga ranar 24 ga watan Mayu .

An hada Manchester United da kungiyar kwallon kafa ta FC Rostov da ke Rasha a matakin sili daya kwale na gasar Europa League.

United, wadda masharhanta ke yi wa kallon masu samun nasara a gasar, su kadai ne kungiyar kwallon kafa ta Birtaniya da ke cikin gasar cin kofin Europa League.

Kungiyar ta Jose Mourinho ta doke Saint-Etienne 4-0 cikin wasanni biyu a mataki na baya.

"Mummunan hadi ne a ko wane mataki," inji Mourinho. "Yana da nisa - kuma yana da yawa, kuma ya zo a wani lokaci mara kyau."

Za a buga wasanni biyu tsakanin kungiyoyin ranar Alhamis 9 ga watan Maris, da kuma 16 ga watan Maris.