Rooney na tare da United-Mourinho

Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mourinho ya ce Rooney zai tsaya a United

Dan wasan gaban Manchester United, Wayne Rooney, zai buga wasan karshe na gasar cin kofin EFL inda United za ta kara da Southampton, inji kociya Jose Mourinho.

Keftin din tawagar England in bai buga wasannin United uku da suka wuce ba bayan ya ji ciwo a guiwa.

Mourinho ya ce: "Yana cikin koshin lafiya, ya fara atisayi da 'yan tawagar. Ya yi furucin tsayawa a nan a lokacin da ya dace."

Wanda ya fi zura wa United kwallo a raga ya fitar da wata sanarwa ranar Alhamis inda ya ce yana fatan kasancewa tare da kungiyar gasar firiyimiyar zuwa karshen kakar bana.