'Ba 'yan gudun hijira ne kadai a sansanoni masu zaman kan su ba'

Sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin 'yan Najeriya da muhallansu, inda yawanci ke rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira

A Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, mazauna sansanonin 'yan gudun hijira ma su zaman kan su da ke birnin Maiduguri, sun koka da rashin samun wani tallafi daga gwamnati.

Irin halin da suke ciki na rashin samun tallafi daga hukomomi da kungiyoyi masu zaman kansu daya daga cikin matsalolin da suke fama da su.

Galibin wadannan 'yan gudun hijar dake zaune a sansanoni daban-daban a cikin birnin sun samu taimakon matsugunan ne daga wasu mutanen gari .

Yan gudun hijirar a wasu lokutan kan samu agaji daga wasu kungiyoyi masu zaman kan su na kasashen waje,sai dai can ba rasa ba, suke samun irin wannan tainako.

Amma kuma tallafin ba ya isar su kamar na saauran 'yan gudun hijrar dake sansanonin da gwamnati ta kafa.

Jami'an kula da bayar da agaji ga jama'a a matakin jiha da kuma na tarraya sun nuna cewa gwamnati na bakin kokarinta game da wannan lamari.

To sai dai wasu basu bayyana kansu ba a matsayin 'yan gudun hijira,wannan na daya daga cikin abubuwan da ke kawo hakan.

A ziyarar da wata tawagar BBC ta kai jihar Bornoa kwanakin baya-bayan nan, ta shiga wasu daga cikin wadannan sansanoni don ganin halin da suke ciki.

Sun kuma tattauna da shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Bornon SEMA, Injiniya Ahmed Satomi kan wadannan matsaloli da koke-koke na yan gudun hijirar.

Satomi ya ce yawancin irin wadannan sansano ni gwamnati ba ta san da su ba, babu kuma wata hukuma ko kungiyar agaji wadda ke aiki tare da gwamnatin Najeriya tun daga matakin tarayya har jiha da suka san da zaman su.

Ya kara da cewa a wasu lokutan ma, ba 'yan gudun hijira ne ke zaune a sansanonin ba mutanen gari ne da rayuwa ta musu kunci, ko kudin hayar gidajen su ya kare su ke fadawa wuraren dan samun tallafin.

''Ko a kwanakin baya mun gudanar da bincike a sansanoni masu zaman kansu saboda korafin rashin tallafin ya yi yawa, amma abin mamaki ni da kaina na ga mutane da dama da na sa ni har da 'yan mata da ba 'yan gudun hijira ba ne'', in ji shi.

Labarai masu alaka