Trump ba zai halarci liyafar 'yan jarida ta bana ba

Donald Trump
Bayanan hoto,

Tun bayan shan rantsuwar kama aiki, shugaba Trump ke 'yar tsama da 'yan jarida, ya kuma zarge su da yada labaran karya

Shugaba Donald trump ya ce ba zai halarci liyafar cin abincin dare tare da 'yan jarida da aka saba yi ba duk shekara a fadar White House a wani mataki na kara tsamama dangantaka tsakanin shi da su.

Ko a ranar juma'a da ta gabata, an hana gidajen jarida irin BBC, da CNN da New York Times shiga wurin da mai magana da yawun gwamnati Sean Spicer ya ke tattaunawa da manema labarai.

Sai dai kuma kungiayr manema labarai ta fadar, wadda ita ke shirya liyafar, ta ce bikin da za a yi a watan Afrilu mai zuwa zai nuna yadda aka yi wa kundin tsarin mulkin Amurka kwaskwarima, da baiwa 'yan jarida 'yan cin gudanar da aikin su.

A kullum dai shugaba Trump kara bata dangantaka tsakanin gwamnatinsa da 'yan jarida ya ke yi, tare da zargin su na yada labaran karya, ya kuma kira wasu daga cikinsu a matsayin makiyan Amurka.

kusan shekaru 100 kenan da ake kungiyar 'yan jarida ke shirya biki irin wannan a duk shekara, wanda bisa al'ada ya kamata shugaban kasa ya halarta.